Hebrews 13

1Bari kaunar ‘yan’uwa ta cigaba. 2Kada ku manta da karrama baki, domin ta wurin yin haka, wasu suka marabci mala’iku ba tare da saninsu ba.

3Ku tuna da wadanda ke cikin kurkuku, kamar dai kuna tare da su cikin wannan hali. Kuma ku tuna da masu shan azaba kamar tare kuke cikin wannan hali 4Bari kowa ya girmama aure, bari kuma a tsarkake gadon aure, gama Allah zai shar’anta fasikai da mazinata.

5Bari halinku ya kubuta daga kaunar kudi. Ku dangana da abubuwan da kuke dasu, domin Allah da kansa yace, “Bazan barku ba, ba kuma zan yashe ku ba.” 6Bari mu zama da dangana domin mu sami gabagadin cewa, “Ubangiji ne mai taimakona, ba zan ji tsoro ba. To me mutum zai iya yi mani?”

7Ku fa lura da wadanda ke shugabanninku, wadanda suka horar da ku cikin maganar Allah, kuma ku lura da sakamakon rayuwarsu, ku yi koyi da bangaskiyarsu. 8Yesu Almasihu daya ne a jiya, da yau, da har abada.

9Kada ku kauce zuwa ga bakin koyarwa daban daban, domin yana da kyau zuciya ta ginu ta wurin alheri, amma ba da dokoki game da abinci ba, wadanda basu taimaki wadanda suka kiyayesu ba. 10Muna da bagadin da wadanda ke hidima a cikin alfarwa basu da ikon su ci daga bisansa. 11Babban firist na shiga wuri mai tsarki da jinin dabbobin da aka yanka, hadayar zunubai, amma namansu a kan kai bayan sansani a kone shi.

12Domin haka Yesu shima ya sha wahala a bayan kofar birnin, domin ya tsarkake mutane ta wurin jininsa. 13Domin haka bari mu tafi gare shi a bayan sansani dauke da kunyarsa. 14Domin bamu da wani birni dawwamamme a nan. Maimako haka muna bidar birni dake zuwa.

15Ta wurin sa kuma, bari kullum mu mika hadayu na yabo ga Allah, yabon kuwa shine kalmomin bakinmu da ke daukaka sunansa. 16Kada kuma mu manta da yin nagarta da kuma taimakon juna, domin Allah na farin ciki sosai da irin wadannan hadayun. 17Ku yi biyayya da sadaukarwa ga shugabanninku, domin suna aikin tsaro a kanku saboda rayukanku, kamar wadanda zasu bada lissafi. Kuyi biyayya gare su saboda su yi aikin lura daku cikin farin ciki, ba da bakin ciki ba, don in su yi da bakin ciki ba zai amfane ku ba.

18Kuyi mana addu’a, domin mun tabbata muna da lamiri mai tsabta, kuma muna burin muyi rayuwar dake daidai cikin dukkan al’amura. 19Kuma ina karfafa ku dukka kuyi haka, domin in sami dawowa gareku da sauri.

20To bari Allahn salama, wanda ya tada babban makiyayin tumakin nan daga matattu, Ubangijinmu Yesu, ta wurin jinin madawwamin alkawari, 21ya kammala ku da dukan abu mai kyau domin ku aikata nufinsa. Bari yayi aiki a cikinmu wanda zai gamshe shi sosai. Ta wurin Yesu Almasihu, bari daukaka ta tabbata gare shi har abada. Amin.

22‘Yan’uwa, yanzu dai ina karfafa ku, da ku jurewa takaitacciyar maganar karfafawar da na rubuto maku. 23Ina so ku sani an saki dan’uwan mu Timoti, tare da shi zan zo in gan ku idan ya iso da sauri.

24Ku gaida shugabanninku dukka da kuma dukkan masu bada gaskiya. ‘Yan’uwa daga can Italiya suna gaishe ku. 25Bari alheri ya kasance tare daku dukka.

Copyright information for HauULB